An zargin wani Dan shekaru casa in da hudu dayiwa yar shekaru sha uku da haifuwa fyade a jahar Adamawa.
Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta cika hanu da wani mutum mai shekaru casa in da hudu da haifuwa yayiwa yar shekara sha uku da haifuwa fyade a cikin karamar hukumar Ganye dake jahar Adamawa.
Kakakin rundunan yan sanda jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Sanarwar ta baiyana cewa mutumin mai suna Muhammadu Abubakar dan shekara casa in da hudu yana zaune ne a unguwar Tappare dake cikin karamar hukumar ta Ganye. Wanda kuma yana aiyana kansa dacewa mai maganin gargajiyane, inda yake yaudaran yaran mata dacewa zai baau minti da dai sauransu. Inda yake amfani da wannan damar wajen cin zarafinsu.
Bincike ya nuna cewa an kama wanda ake zargine biyo bayan raunin da yarinyar taji wanda hakan yasa mamanta ta tambayeta ina ta samu wannan rauni bayan ta gayawa mamannatane sai ta garzaya ofishin yan sanda dake Ganye domin kai rahoton lamarin. Hakan yasa ba ayi da wasaba wajen kama wanda ake zargin.
A yanzu haka dai kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya bada umurnin gudanar da binciken gaggawa dangane da lamarin kuma da zaran an kammala bincike za a gurfanar da shi gaban kotu domin ya fuskanci shariya.
Kwamisina ya kirayi al umma dake fadin jahar musammanma iyaye da sukace masu maida hankali kan yaransu a koda yaushe domin kaucewa irin wadannan batagari.
A cewarsa rundunan tana iya kokarinta domin ganin ta takile dukkanin aiyukan bata gari a tsakanin jama a.
Comments
Post a Comment