Gidauniyar Attarahum ta bukaci hadin kan kafafen yada labarai wajen gudanar da aiyukansu.
Gidauniyar Attarahum ya nemi hadin Kai kafafen yada labarai dake fadin jahar domin ganin sun cimma burinsu na taimakawa Al umma dake fadin jahar baki daya.
Shugaban Gidauniyar ta Attarahum a jahar Adamawa Mallam Mukhatar Dayyib ne ya baiyana haka a lokacinda suke ziyarata kafafen yada labarai dake nan yola.
Mallam Mukhatar Dayyib yace Gidauniyar ta Attarum Yana maida hankali wajen taimakawa marassa galihu, marayu dama sauran mabukata.
Yace sun dauki matakin ziyarta kafafen yada labarain ne domin neman goyon bayansu domin ganin sun samu nasaran gudanar da aiyukansu na taimakawa jama a.
Malam Dayyib ya Kuma baiyana cewa Gidauniyar na da rassa a dukkanin kananan hukumomi ashirin da Daya dake fadin jahat ta Adamawa harma da anguwanin dake cikin kananan hukumomin.
Don haka Gidauniya na tsaye daram domin ganin an taimakawa Al umma dake cikin da wajen jahar ta Adamawa
Ya Kuma nuna jindadinsu da godiyar dangane da irin tarya karamci da kakafen yada labarain suka yi musu wanda hakan ya Kara musu kwarin gwiwar cigaba da aiyukansu yadda ya kamata.
A jawabensu manajojin gadajen Rediyo Fombina Alhaji Dahiru Garba Muhammed Wanda shugabar sashin kasuwanci Hajiya Sa adatu Murtala ta wakilta. da na Nass Alhaji Musa Waziri Hardawa sun yaba da irin wannan ziyara da suka kawo tare da tabbatar musu da cewa a shirye suke su basu hadin Kai da goyon baya domin ganin an samu nasara da cigaban gudanar da aiyukansu.
Comments
Post a Comment