Gwamnan jahar Gombe ya amince da nadin sakataren da na musamman.
Gwamnan jahar Gombe Muhammed Inuwa Yahaya ya amice da nada Mohammed Usman Shanu a matsayin sakatarensa na musaman.
Muhammed Ahmed Shaunu ya maye gurbin tsohon sakataren Ahmed Kasimu Abdullahi wanda kawo yanzu an nadashi a matsayin shugaban ma aikatan jahar na riko tun a watan mayun wanan nan shekara.
Kafin nadashi a matsayin sakatare na musamman Muhammed Shanu shine Babban darektan aiyuka a ofishin sakateren gwamnatin jahar ta Gombe.
Gwamnan kuma ya amice da Alhaji Ahmed Kasimu Abdullahi a matsayin shugaban ma aikatan jahar na riko kuma zai fara aikne a nan take.
Comments
Post a Comment