Gwamnatin jahar Gombe ta lashi takwabin bunkasa harkokin kasuwanci a jahar.

Gwamnanatin jahar Gombe ta lashi takwabin ganin an bunkasa harkokin kasuwanci domin amfanar al ummar jahar baki daya. Gwamnan jahar ta Gombe Muhammed Inuwa Yahaya ne ya bauyana haka a lokacinda ya marabci tawagan kamfanin Lafarge Africa PLC.a ziyaran da suka kai masa. Tawagan karkashin jagorancin group managing darecta kamfanin Mr Lolu Alade tare da managing darectan kamfanin simitin Ashaka da dai sauransu ne suka kaiwa gwamnan ziyara. A tattaunawa da sukayi dai sun tsaida shawaran hada karfi da karfe domin hada kai da gwamnatin jahar Gombe da kamfanin siminti domin ganin an samu cigaba a fannoni daban daban a fadin jahar baki daya. Taron tattaunawar ya samu halartan sakataren gwamnatin jahar ta Gombe Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi tare da kwamishinan ciniki a jahar Barista Zubair Muhammed Umar kuma ciroman Gombe.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE