Hukumar dake yaki da fataucin mutane tayi gargadi da a lura da masu safaran mutane a jahar Adamawa.
Hukamar dake yaki da safaran mutane ta kasa NAPTIP shiyar jahar Adamawa ta gargadi mazauna jahar Adamawa da sukasance masu sanya idi da Kuma maida hankali wajen aiyuka masu safaran mutane a Koda yaushe.
Shugaban hukumar ta NAPTIP a jahar Adamawa Malam Adamu Ibrahim Bah ne yayi wannan gargadi a zantawarsa da manema labarai a yola.
Shugaban yace hukumar yanayin dukkanin abinda zata iya domin tabbatar da ganin an dakile aiyukan masu safaran mutane a fadin jahar baki daya.
A cewarsa dai yanzu hakama hukumar ta fara gangamin wayarwa Al umma Kai dangane da matsalar ta safaran mutane a wurare daban daban da suka hada da masallatai, makami u da dai sauransu.
Ya Kuma baiyana cewa gwamnati na iya kikarinta na ganin an dakile aiyukan safaran mutane a fadin Najeriya
Harwayau shugaban hukumar Malam Adamu yace hukumar ta NAPTIP zata hada Kai da sauran hukumomin tsaro wajen yin aiki tare a wani mataki na kawar da aiyukan safaran mutane a tsakanin Al umma baki daya.
Comments
Post a Comment