Kasar Jamus zata taimakawa karamar hukumar Michika dake jahar Adamawa.
Karamar hukumar Michika tana Daya daga cikin kananan hukumomi da ta fuskanci rikin boka Haram a yankin Arewacin jahar Adamawa.
Karamar hukumar Michika dai tanadaga cikin kanan hukumomi suke gudanar da harkokin noma kiwo dama kasauwanci daban daban, mata da dama a karamar hukumar ta Michika suna gudanar da harkokin noma dama kasuwanci daban daban.
Hakan yasa gwamnatin kasar Jamus ta kudiri aniyar taimakawa karamar hukumar domin tada komadan tattalin arziki da ta samu sakamokon matsalar tsaro.
A wurin bikin kaddamar da bada taimakon da za ayiwa angwani goma sha shida dake karamar hukumar ta Michika a jahar Adamawa. Darectan GIZ a Najeriya Da ECOWAS Dr Markus Wagner tare da farkon sakatare ofishin jakadancin Jamus a Najeriya dake Abuja Susane Schroder sukace Samar da wadaceccen abinci da tallafawa zai taimaka wajen cigaban yankin yadda ya kamata.
Shima da yake nashi jawabi manager Nigeria Energy Support Programme Duke Benjamin yace tun a shekara ta dubu biyu da ashirin da biyu ne aka shiga tsakanin domin taimakawa Al Umar karamar hukumar ta Michika.
Suma a jawabensu daban daban shugaban hukumar tsare tsare a jahar Adamawa Mery Paninga da shugaban karamar hukumar ta Michika Amos Dirambi sun baiyana cewa yin amfanin da kimiya zai taimakawa wajen bunkasa harkokin cigaban karamar hukumar, tare da Kiran wadanda suka anfana da Shirin da suyi amfani da abunda suka samu ta hanyar da ta dace domin samun cigaba.
Hakimin karamar hukumar ta Michika Ngida Ngirda Zakawa ya baiyana farin cikinsu da Jin dadinsa dangane da wannan taimakon da akayiwa karamar hukumar ta Michika.
Tun da farko a jawabinsa mukaddashin darektan OXFAN a Najeriya Hamza Tijjani Ahmed ya baiyana cewa ana gudanar da irin wadannan aiyukane da zummar kawo karshen matsanancin rayuwa da mazauna karamar hukumar ke ciki.
Comments
Post a Comment