Kwamiti rarraba kayakin tallafi na jahar Gombe ya kaddamar da fara rarraba kayakin tallafi a jahar Gombe

Kwamitin rarraba kayakin tallafi a jahar Gombe biyo bayan matsanancin tattalim arziki da aka shiga bayan cire tallafin maifetur da gwamnatin tarayya tati. Ya kaddamar da fara rarraba tallafin kayakin abinci da sauransu a cikin karamar hukumar Kwami dake jahar ta Gombe. Gwamnan jahar ta Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ne ya jagorancin kaddamar da fara rabon kayakin a karamara hukumar ta Kwami. Gwamnan wanda mataimakinsa Manassah Jatau ya wakilta yace gwamnatinsa zatayi dukkanin maiyiwa domin fadada aiyukanta wajen taimakon Al ummar dake fadin jahar baki daya. Gwamnan yace wahalar da jama a suka shiga sakamokon cire tallafin maifetur yayi sanadiyar samarwa jama a damuwa sosai don hakane gwamnati taga ya dace ta tallafa domin ganin al umma sun samu saukin rayuwa. Ya kuma kirayi al umma musammanma matasa da su rungumi harkokin noma dama koyon sana o i dogaro da kai wanda acewarsa haka zaitaimaka wajen rage radadin wahala da ake fuskanta. Shugaban kwamitin rarraba kayakin kuma Babban sakatare na hukumar agajin gaggawa ta jahar Gombe (SEMA) ya baiyanawa taron cewa gwamnan ya nuna damuwarsa dangane da halin kuncin rayuwa da jamma a ke cikine yasa ya amince da tallafawa al umma dake fadin jahar. Ya kara da cewa mutane dubu biyu da dari uku da saba in ne zasu amfana da taimakon a cikin karamar hukumar ta Kwami harma da mutane goma goma daga runfunan zabe dari biyu da talatin da bakwai dake karamar hukumar ta Kwami.
Ya kirayi kwamitin da ya gudanar da rarraba kayakin yadda ya kamata da suka hada da Takin zamani, shinkafa, taliya, da kuma goran maganin feshi dake duke Lita biyu. A nasu jawabai mataimakin shugaban jam iyar A P C na jahar Gombe Alhaji Baba Abuja da kuma shugaban riko na karamar hukumar Kwami Alhaji Ibrahim Buba Makama sun godewa gwamnan bisa maida hankali da yayi ga al ummar karamar hukumar ta Kwami . Hakimin Kwami kuma ajiya Gombe Alhaji Aminu Haruna Abdullahi yace al ummar masarautar ta Kwami zasu cigaba da baiwa gwamnatin hadin kai da goyon baya domin ganin ta cimma burinta na tallafawa jama a. Sakataren gwamnatin jahar ta Gombe Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi yace gwamnan na bukatan goyon bayan sarakuna domin ganin gwamnatin ta kaucewa abun kunya. Yace gwamnati tana da tsare tsare da zaiyi la akari da sarakunan gargajiya domin ganin an samu kyakkawar gwamnati dama cigaban al ummar jahar baki daya. Hakimin na Kwami Alhaji. Haruna Abdullahi ya yabawa gwamnan tare da yin alkawarin cewa masarautar zata bada cikekken goyon bayanta ga gwamnatin domin samun damar gudanar da aiyukan cigaban jahar. Shugaban Ma aikatan jahar na riko Alhaji Ahmed Abdullahi Kasimu da manyan sakatarorin ma aikatu daban daban sun halarci taron rarraba kayakin tallafin .

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.