Rundunan yan sanda a jahar Adamawa ta raba Jami anta biyu da aikinsu.

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ya raba Jami an yan sanda biyu da aikinsu biyo bayan samunsu da lafin kisan Kai.
Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yola.
Jami an yan sanda da lamarin ya shafa dai sun hada da Ahmed Suleiman Mai mukamin isfeta, da Mahmood Muhammed Mai mukamin kostabul Kuma dukkaninsu suna aikine a ofishin rundunan dake Dumne dake cikin karamar hukumar Song a jahar Adamawa.
Biyo bayan bincike da rundunan ta gabatar ya samu Jami an da lafin kisan Kai don haka an Koresu da aiki kamar yadda dokan rundunan Yan sandan na sashi 370 Wanda akayiwa gyara a shekara ta 2020 na cewa duk Jami in Dan sanda da aka samu da lafin kisa za a hukuntashi tare da koransa daga aikin Dan sanda. Saboda haka bayan an Koresu za a gurfanar dasu gaban kotu domin su fuskanci shariya. Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya gargadi Jami an Yan sanda da sukasance masu gudanar da aiyukansu bisa doka domin kaucewa fushin rundunan yan sandan na Najeriya .

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE