Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta samu nasaran kama matasa hudu da ake zargi da dayin amfani da yanan gizo domin sace kudaden Jama a.
Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta kama wasu matasa hudu dake amfani da yanan gizo wajen kwashewa Jama a kudadensu daga asusun ajiyarsu dake Bankuna.
Sashin binciken manayan laifuka na rundunan wati CID ne sukayi nasaran kama matasa wadanda dukkaninsu suna zaune ne a Anguwar Shagari rukunin na biyu dake cikin karamar hukumar yola ta kudu a jahar Adamawa.
Kakakin r rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yola.
Sanarwan ta baiyana cewa kawo yanzu dai bincike ya nuna cewa wadanda ake zaigi suna aikata lafin haka tun daga shekara ta 2022.
Da wannan ne kwamishinan dan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola yasha alwashin dakile duk wasu laifuka a fadin jahar, kuma yace da zaran an kammala bincike kan wadanda ake zargi za a gurfanar dasu gaban kotu domin su fuskanci shariya.
Ya kuma kirayi al umma da su taimakawa rundunan ta sanya ido kan masu aikata lafuka, da zaran duk wanda ya gansu ya kai rahotonsu zuwa ofishin yan sanda dake kusa.
Comments
Post a Comment