Rundunan yan sandan jahar Bauchi ta damke wani makayayi da ake zargi da sare hanun manomi.

Rundunan yan sanda a jahar Bauchi ta samu nasaran cafke wani Mai suna Adamau Ibrahim Dan shekara sha biyar da haifuwa Wanda ke kauyen Jital akan hanyar da ta hada Jihar Gombe da Bauchi.bisa zarginsa da sare hanun wani manomi. Kakakin rundunan yan sandan na jahar Bauchi SP Ahmed Muhammed Wakil ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a jahar Bauchi. A binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa sau da dama Wanda ake zargin Yana shiga gonar Wanda aka jiwa raunin da shanunsa. Lamarida yasa Mai gonar ya Kai kukansa ga baban Wanda ake zargi inda ya shaida masa cewa ya shiga gonarsa da dabbibi Kuma amsa barna sosai a gonar. Harwayau bincike ya nuna cewa a ranan 24-8+2023. Wanda ake zargin dauke da sanda da Kuma addarsa ya kusa gonar tare da lalata amfanin gonar. Biyo bayan haka ne Mai gonar ya umurceshi da ya fita daga gonarsa, sakamokon hakane Wanda ake zargin ya zare addarsa ya sare hanun hagundin Mai gonar.
Daga samun wannan labarine sai Kwamandan ofishin Yan sanda dake yankin cikin garin na Bauchi ya garzaya inda lamarin ya faru inda nan take aka tsare Wanda ake zargi Kuma aga garzaya da manomin zuwa asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa dake jahar Bauchi domin yin jinya. Kawo yanzu dai kwamishinan yan sandan jahar Bauchi Auwal Musa Muhammed ya gargadi makiyaya da su nisanta kansu da shiga gonakain Al umma domin kaucewa tashin hankali. Ya Kuma bada umurnin gudanar da bincike tare da gabatar da Wanda ake zargin gaban kotu domin ya fuskanci sahariya .

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE