Akalla mata hamsine wadanda ke dauke da cutar yoyo fitsarin akayiwa fida kyauta a jahar Gombe.

Daga Ibrahim Abubakar Gombe
An kirayi magidanta da sukasance suna baiwa iyalen su kula na musamman a lokacinda suke dauke da juna biyu domin kaucewa kamuwa da cutar yoyon Fitsari wato VVF. Shugaban kungiyar dake yaki da cutar yoyon fitsari wato Gidauniyar Fistula a Najeriya (FFN) malam Musa Isa ne yabaiyana haka a lokacinda ya jagoranci yiwa mata dake dauke da cutar yoyon fitsarin kyauta a jahar Gombe. Gidauniyar ta fistula tare da hadin gwiwar asusun jama a na majalisar dinkin duniya UNFPA da kuma NORWEGIAN GOVERNMENT sunyiwa mata akalla hamsin fidar cutar yoyon fitsari kyauta wandama tunin aka sallamesu daga aaibitin dake jahar Gombe. Matan wadanda suka fito daga sassa daban daban dake fadin jahar. Kuma an daukai matakin taimaka musu ne duba da irin wahalar rayuwa da suka tsnci kanau a ciki biyo bayan kamuwa da cutar na yoyon fitsari. Dr Sa ad Idris she nema ya jagiranci likitocin fidar yoyon fitsari ya baiyana cewa an samu nasaran yiwa mata hamsin fida cutar yoyon fitsari ba tare da matsalaba. Ya kuma shawarci mata musammanma wadanda ke dauke da juna biyu da sukasance masu bin shawarwarin likitoci domin inganta kiwon lafiyarsu a koda yaushe. Dubun dubatan mata ne dai ke fama da cutar ta yoyon fitsari a yankin arewacin Najeriya, cutar ta yoyon fitsarin dai na kama matanne biyo bayan yiwa mata aure da wuri da kuma tsawon na kuda talauci da dai sauransu. A yayinda cutar ke yin sanadiyar salwatar rayukan mata da dama.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.