Alhaji Usman Abubakar ya jajantawa iyalen wadanda suka gamu da ajalinsu sakamokon kifewar da kwale kwale yayi a kan kogin Rugange.

Alhaji Usman Abubakar Wanda akafi sani da Manu Ngurore ya jajantawa iyalen wadanda suka rasa Yan uwansu sakamokon kefewar kwale kwale a ruwan Njuwa dake rugange a karamar hukumar yola ta kudu a jahar Adamawa. Alhaji Manu Ngurore ya baiyana lamarin a matsayin Babban rashine ga Al ummar jahar Adamawa ba ga rugange Ka waiba. Ya Kuma yiwa adu ar Allah madaukakin sarki ya jikan wadanda suka rasu ya gafarta musu. Wadanda suka jikkata Kuma Allah ya basu sauki. Ya Kuma Kara da cewa Allah ya baiwa Yan uwan wadanda suka mutu jimre hakurin rashin da sukayi Harwa yau Allah Manu Ngurore ya jajantawa iyalen Bello Liman Wanda Shima ya rasu jiya biyo bayan gajeruwan jinya da yayi yayi Adu ar Allah ya jikanshi da rahama. Ya Kuma jajantawa gidan rediyo Nass bisa rashin ma aikacinsu da sukayi wato Bello Liman. Bello Liman kafin rasuwarsa dai ma aikacin gidan rediyo Nass ne.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE