An bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da aniyarta na baiwa Jami o I cin gashin kansu.

An kirayi gwamnatin tarayya da ta janye aniyarta na baiwa Jami o I cin hashin kansu domin kaucewa yabarbarwar ilimi a fadi kasan nan. Shugaban kungiyar malamain Jami o I a Najeriya ASUU shiyar Jami ar Modibbo Adama dake yola Dr El Maude Jbril ne ya yi wannan kira a zantawarsa da manema labarai a yola. Dr El Maude irin cin gashin da yakamata a baiwa Jami o I shine basu damar daukan ma aikata da suka kware da Kuma tsara yadda zasu gudanar da lamaransu yadda ya kamata. Don haka bai kamata ace gatsau kawai gwamnati tace zata baiwa Jami o I cin gashin kansuba. Kuma kamata yayima ta zauna da Jami o I su tattauna kafin daukan mataki da yakamata. Dr El Maude yace daukan mataki irin wannan zai kawo komabaya matuka dangane da koyarwar Jami o I a fadin Najeriya Dan haka gwamnatin tarayyar ta zauna tayi tunani Mai zurfi dangane da wannan aniyatata. El Maude yace wannan ya nuna cewa Rance da gwamnatin tarayya tace zata baiwa dalube domin karatu ashe zancene kawai saboda haka ya kamata gwamnatin tarayyar ta gudanar da aiyukan cigaban Jami o I domin ingantasu. Ba wai ta baiwa Jami o I cin gashin kansuba. Saboda haka suna Jan hankali gwamnatin tarayya da ta duba ta sake yin nazari domin kaucewa abunda zaiyiwa harkokin ilimi tarnaki.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.