An bukaci masu anfani da kwale kwale da su kasance suna maida hankali wajen anfani da kwale kwale.

An shawarci masu amfani da kwale kwale da sukasance masu yin daka tsantsan a duk lokacinda suke gudanar da aiyukansu domin kaucewa aukuwar hatsari akan koguna. Sarkin ruwan Gerio Alhaji AbdulRazak Abubakar ne ya bada wannan shawara alokacin da yake tsokaci dangane da hatsarin kwale kwale da aka samu a wasu kananan hukumomi dake jahar Adamawa Alhaji AbdulRazak Abubakar yace ya kamata matuka kwale kwale su san yawan mutane da zasu rinka deba a cikin kwale kwale da Kuma yawan kaya da zasu rinka lodawa. Alhaji AbdulRazak yace kowane kwale kwale akwai daidain kayan da yakamata a sanya masa dama yawan mtane da yakamata a diba, don haka masu amfani da kwale kwalen su maida hakali sosai wajen aiki da kwale kwalen a Koda yaushe. Ya Kuma kirayi gwamnatin jahar da sukasance masu Sa ido akan harkokin yadda ake gudanar da aiyukan kwale kwalen a fadin jahar baki Daya. Domin ganin an samu cigaba yadda yakamata. In za a iya tunawa dai a kwanan nan ne aka samu haduran kifewar kwale kwale akan koguna da suka hada Dana Rugange a cikin karamar hukumar yola ta kudu Dana Gurin a cikin karamar hukumar Fufore dukkaninsu a jahar Adamawa, lamarin da yayi sanadiyar asaran rayuwa dama jikkata da dama tare Kuma da bacewar wasu.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE