Àn bukaci masu rike da masarautun gargajiyà da su bada tasu gudumawa wajen wanzar da zaman lafiya dama hadinkan Al umma.
An kirayi masu rike da masarautun gargajiyà da sukasance masu gudanar da yin dukkanin abunda zaikawa hadin Kai dama zaman lafiya a tsakanin Al umma bak Daya.
Hakimin Girei Kuma Uban Doman Girei Dr Ahmed Mustafa ne yayi wannan kira a lokacinda ya marabci tawagan ziyaran godiya da aka Kai masa a fadarsa dake karamar hukumar ta Girei a jahar Adamawa.
Babban sakataren Hukumar jindadin Alhazai na jahar Adamawa Mallam Salihu Abubakar nedai ya jagoranci tawagan Kai ziyaran godiyar boyon bayan da ya baiwa Alhaji Adamu Ahmed sarautar wakilin Alhazain karamar hukumar ta Girei.
Hakimin yace masu rke Sa masarautun gargajiyà suna da muhimmiyar rawa da zasu iya takawa wajen Samar da zaman lafiya da Kuma cigaban kasa. Don haka akwai bukatar Suma su bada tasu gudumawa wajen gina kasa.
Ya Kuma baiyana cewa bisa cancantarsa da Kuma irin gudumawar da ya bayarwa Al ummarsa ne yasa ya bashi wannan sarautar na wakilin Alhazai don haka ya zama wajibi ya zage damtse domin gudanar da aiyukan cigaban yankin na karamar hukumar Girei dama jaha baki Daya.
A cewar Hakimin dai tunda wakilin Alhazai ya gudanar da aiyukansu a karamar hukumar ta Girei ba a taba samunsa da wani laifiba saboda ya gudanar da aiyukansane bilhakki da gaskiya domin samun cigaban karamar hukumar ta Girei.
Shima da yake jawabinsa Alhaji Adamu Ahmed Wanda Kuma shine sabon wakilain Aljazain karamar hukumar ta Girei ya mika gidiyarsa ga Allah Madaukakin sarki tare Kuma da godewa Hakimin na Girei bisa wanna mukamin sarautar da ya bashi na wakilain Alhazain Girei.
Alhaji Adamu Ahmed ya Kuma tabbatar da cewa a shirye yake ya baiwa masarautar karamar hukumar ta Girei hadin Kai da goyon baya domin ganin an samu cigaban masarautar dama karamar hukumar ta Girei baki Daya.
Ya Kuma tabbatarwa Hakimin Kuma Uban Doman Girei cewa ba zai bashi kunyaba wajen yin aiyukan da zai kawo cigaban masarautar dama Al ummar Girei.
Da wannan nema yake kira ga daukacin Al ummar karamar hukumar ta Girei da sukasance masu baiwa masarautar ta Girei hadin Kai da goyon baya. Da Kuma cigaba da.ad o i domin Neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen karshen dukkanin kalubalen tsaro a fadin jahar dama kasa baki Daya.
Shima anashi bangare tsohon Babban sakatare a harkokin aiyasa Musa Ahmed Gaude shikàm zaiyano tarihin Wakilin Alhazain na Girei yayi inda ya baiyana cewa ya fara karatunsa na ilimantare na sakandare a karamar hukumar ta Girei kana daga bisani ya wuce zuwa A T C Song kana ya dawo Jami ar Modibbo Adama dake nan yola.
A bangaren aiyuka kuwa wakilin Alhazain na Girei ya gudanar da aiyuka daban daban daga matakin karamar hukumar ta Girei har zuwa matakin jaha na baya bayannan ya rike shugaban sashin shin gudanar da bincike da dabaru a hukumar Jin dadin Alhazai na jahar Adamawa kafin na Kafin nan Kuma ya rike Jami in tsare tsaren aikin jajjin karamar hukumar ta Girei.
Dayake nashi jawabi Wanda ya jagoranci Kai ziyaran godiya Shugaban hukumar Jin dadin Alhazai a jahar Adamawa Kuma sarkin turawan Gurin, wakilin asibitin Shelleng. Mallam Salihu Abubakar yace Alhaji Adamu Ahmed ya cancanci sarautar na wakilain aAlhazain karamar hukumar Girei, saboda haka ya yabawa Hakimin na Girei bisa wannan sarautar da ya baiwa Alhaji Adamu Ahmed.
A cewasa Alhaji Adamu kwararrrne wajen gudanar da aiyukan da zai kawo cigaban dama hadin Kai a tsakanin Al umma don haka Hakimin baiyi zaben tumun dareba ya zabe gwarzo wajen yin duk abinda zai kawo zaman lafiya.
Ziyaran dai ya samu rakiyar Jama a da dama wadanda suka fito daga ciki da wajen karamar hukumar ta Girei.
Comments
Post a Comment