An karrama kawamishinan Yan sandan jahar Adamawa da wasu Jami ai biyu.

An yabawa rundunan yan sandan jahar Adamawa bisa kokarinta na inganta tsaro dama kare rayuka da dukiyoyin Al umma baki daya. Shugaban kungiyar Daliben Arewacin Najeriya wato GAMJI kwamuret Umar D Afkawa ne yayi wannan yabao a lakacinda yake jawabi a wurin bikik karrama kwamishinan yan sanda da PPRO da kwamandan Crack wanda ya gudana a ofishin kwamishinan yan sandan dake ahelkwatar rundunan daka yola. Kwamuret Umar D Afkawa yace rundunan karkashin jagorancin kwamishinan yan sandan a jahar Adamawa Afolabi Babatola ya taka rawan ganin wajen samar da tsaro mai inganci a tsakanin jama a musammanma daukan matakai da yakeyi akan masu aikata lafuka daban daban da suka hada da fashi da makami, shila, garkuwa da mutane da dai sauransu.
Kwamishinan ya taka rawan ganin wajen gudanar aiyukan da zaikawao zaman lafiya a tsakanin al umma don hakanema kungiyar daluben taga ya dace ta karrama shuwagabanin rundunan domin kara musu kwarin gwiwa cigaba da kare rayuka dama dukiyoyin al umma. Da wannan ne yake kira ga kwamishinan yan sandan da ya kara zage damtse da kaimi wajen yin dukkanin maiyiwa domin dakile aiyukan ta addanci a fadin jahar baki daya. Baya ga kwamishinan yan sandan Afolabi Babatola da aka karrama. An karrama kakakin rundunan yan sandan wato SP Suleiman Yahaya Nguroje a matsayin Jigo kakain rundunan yan sandan arewacin Najeriya sai kuma kwamandan rundunan Crack SP Hussani Tijjani Dibal shi kuma a matsayin wakilin tsaro da zaman lafiya.
Kungiyar ta Gamji ta jinjina musu bisa na mijin kokari da sukeyi na takawa bata gari birki da kuma wanzar da zaman lafiya dama samar da tsaro a tsakanin al umma. Da yake jawabi kwamishinan yan sandan na jahar Adamawa Afolabi Babatola ya godewa kungiyar dama membobin kungiyar bisa wannan karramawa da sukayi musu ya kuma tabbatar da cewa rundunan a ashirye take ta dauki dukkanin matakai domin kare rayuka dama dukiyoyin al umma baki daya. Tare da kiran daukacin al umma dake fadin jahar da akoda yauahe sukasance masu taimakawa rundunan da duk wasu bayanai da zai baiwa rundunan damar dakile aiyukan ta addanci a fadin jahar ta Adamawa baki daya. Suma a jawabainsu SP Suleiman Yahaya Nguroje da SP Hussaini Tijjani Dibal sun nuna far in cikinsu dangane da wannan karramawa da akayi musu wanda acewarsu wannan zai kara musu kwarin gwiwan cigaba da gudanar da aiyukan magance matsalar tsaro a tsakanin al umma. Sun kuma tabbatarwa kungiyar cewa rundunan bazatayi kasa a gwiwaba domin ganin al umma sunyi barsci da idonsu biyu a fadin jahar baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE