An kirayi kamfanoni masu zaman kansu da su maida hankali wajen daukan matasa aiki.
A wani mataki na rage aikinyi a tsakanin matasa a Najeriya an kirayi kamfanoni masu zaman kansu da su maida hankali wajen deban matasan aiki domin Samar da zaman lafiya dama cigaba mai daurewa a tsakanin Al umma baki Daya.
Alhaji Auwal Usman Kuma shugaban kamfanin Auwalus Business Concept kana shugaban kungiyar masu sanar P O S a jahar Adamawa ne yayi wannan kira a lokacin da yake jawabi a wurin tantancewar da zasuyiwa matasa domin samar musu da aikinyi.
Alhaji Auwal Usman ya baiyana cewa samarwa matasan aikinyi Wanda acewarsa hakan zai taimakawa matasan rage radadin rashin aiki da suke fama da shi, don haka akwai bukatar a maida hankali wajen samarwa matasan sana o I da zasu dogara da kansu.
Da yake jawabi dangane da dalilimsu na daukan matakin diban matasan Alhaji Auwal yace sun dauki matakin hakane duba da irin yanayi da ake ciki na matsalar rayuwa da Kuma uwa uba rashin aikinyi a tsakanin matasa wanda hakan yasa suke shiga wasu hanyoyi da basu daceba suna aikata mamunan aiki.
Don haka ya kamata kamfanoni masu zaman kansu su kara azama wajen sharewa matasan hawayensu ya Samar musu da aikinyi, dama koya musu sana o I da zasu dogara da kansu.
Ya Kuma kirayi gwamnati da masu hanu da shuni da Suma su Kara kaimi wajen koyawa matasan sana o I da zasu dogara da kansu domin Samar da cigaban Mai daurewa a jaha dama kasa baki Daya
Ya kara da shawartar matasan da Suma su maida hankali wajen Neman sana o I dogaro da Kai domin a cewarsa ba lailaine sai gwamnati ta daukesu aikiba saboda in dabbu yayi yawa baya Jin Mai.
Kawo yanzu dai kamfanin na Auwalus Business Concept na niyar daukan ma aikata akalla talatin a karon farko a wani mataki na rage rashin aikinyi a tsakanin matasa.
Comments
Post a Comment