An kirayi kungiyoyi da gwamnatoci dasu maida hankali wajen aiyukan jinkai.
An kirayi gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu da su maida hankali wajen aiyukan jinkai domin taimakawa marassa galihu dama yan gudun hijira a fadin kasa baki daya.
Mataimakin shugaban kungiyar agaji na Jama atul Nasaril Islam na kasa, kuma shugaban kungiya a jahar Adamawa kana short gaban majalisar addinin musulunci a jahar Adamawa Alhaji Gambo Jika ne yayi wannan kira alokacinda yakeyiwa manema labarai jawabi dangane da ranan agaji ta majakisar dinkin duniya a yola.
Alhaji Gambo Jika yace kungiyar agaji na Jamatu Nasaril Islam ta dade tana taimakawa a bangarori daban daban da zaran bukatar haka ta taso. Wanda hakan yasa kungiyar ta fadada aiyukanta zuwa dukkanin kanana hukumomi aahirin da daya dake fadin jahar Adamawa.
Alhaji Gambo yace don haka yakanata ace masu hanu da shuni dama gwamnatoci dama kungiyoyi masu zaman kansu su dukufa wajen gudanar da aiyukan agaji domin ganin an samu walwala atsakanin al umma.
Ya kuma baiyana cewa majalisar dinkin dunya ne dai ta aiyyana kowace assabar na biyu na watan tara na kowace shekara ne dai a matsayin ranan agaji ta duniya domin dubawa tare da lalubo yanyoyi da zasu taimaka wajen aiyukan jinkai a tsakanin al umma.
Ya kuma yabawa kungiyar agajin ta Jama atul Nasaril Islam bisa jajircewa da takeyi wajen aiyukan jinkai a tsakanin Al umma da zaran wani iftila i ya auku.
Itama anata bangaren Amiran kungiyar agajin a bangaren mata a jahar Adamawa Hajiya Amina Muhammed Bashir tace suna gudanar da aiyukan jinkai da suka hada da bada magunguna, abinci, da dai sauransu.
Ta kuma kara da cewa ko a cikin azumima suna shirya yin tafsiri da karatuttuka daban daban harma da taimakawa marayu dake fadin jahar ta Adamawa.
Comments
Post a Comment