An kirayi mata da sukasance masu shiga harkokin siyasa domin damawa dasu a cikin harkokin gwamnati.

An shawarci mata da sukasance masu shiga a dama dasu a cikin harkokin siyasa domin samun kyakkawar gwamnati dama adalci a tsakanin al umma. Dr Erisa Danladi ce ta baiyana haka a wajen taron kwana daya wanda cibiyar musayar bayanai da cigaban al umma wato DEC ta shirya a jahar Gombe. Dr Erisa wanda itacema bakuwa mai jawabi a wurin taron ta baiyana cewa abinda yake hana mata shiga siyasa domin adama dasu sun hada da rashin kudi, matsalar hangar siyasa da dai sauransu. Tace yana da muhimmanci in aka samu mata suna rike da mukamai daban daban ta kara dacewa in har gwamnatoci a dukkanin matakai zasu baiwa mata kaso talatin da biyar na guraben aiki dama mukamai kamar yadda kotu ta bayar matan zasu samu nasaran samun wakilci a cikin harkokin gwannati.
Ta kuma baiyana cewa yana da muhimmanci a shirya gangamin wayar da kai domin samar da doka da zaibaiwa matan shiga harkokin siyasa, saboda kada jam iyun siyasa suyiwa matan kadanga wajen shiga adama dasu cikin harkokin siyasa. Domin acewarta in ba hakaba tofa za a dauki tsawon lokaci kafin matan su samu wakilci a gwamnati. A jawabinta na bude taro Darectan cibiyar ta DEC Mrs Helen Aba tace mata suna taka muhimiyar rawa wajen raya al umma don haka akwai bukatar baiwa matan dama domin su samu wakilci a cikin harkokin gwamnati.
Shugaban shirye shiryen cibiyar Mr Samuel B Yelmison maraba yayiwa wadanda suka halarci taron daga kungiyoyi daban daban wadanda suka fito daga jihohi Gombe, Bauchi, Borno, da kuma Adamawa tare da gode musu an kuma tattauna batutuwa da dama domin zakulo hanyoyin da zai baiwa matan dama shiga adama dasu a cikin harkokin siyasa. Shugabar sashin tabbatar da adalci a cibiyar Mrs Rachael Luka tace an gudanar da taron ne domin kawo karshen abinda yake hana matan shiga a dama dasu a cikin siyasa tun a matakin farko.
Da take jawabi a madadin wanda suka halarci taron tsohuwar shugabar mata daga yankin kudancin jahar Bauchi Hassana Akila ta nuna jin dadinta da kuma farin cikinta dangane da shirya wannan taro domin acewarta sun koyi abubuwa da dama kum zasuyi amfani da su ta hanya da ta dace domin ganin matan sun taka rawan gani a cikin harkokin siyasar Najeriya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE