An shawarci Al umma da bunkasa harkokin Al adu domin Samar da hadin Kai a tsakanin Al umma.

. An shawarci al umma da su maida hankali wajen kula dama bunkasa harkokin al adu domin samun hadin kai harma da wanzar da zaman lafiya a tsakanin Jama a. Shugaban kungiya baoys brigade a Najeriya shiyar karamar hukumar Girei a jahar Adamawa Mr Joshua Philemon ne ya bada wannan ahawara alokacinda yake jawabi a wurin bikin rawai rawain gargajiya da kungiyar ta shirya a Karamar hukumar ta Gieri a jahar Adamawa. Mr Joshua Philemon yace makasudin shirya wannan biki shine domin musayar fasaha da da a a tsakanin membobin kungiyar ta Boys brigade da kuma samun damar koyon Al adu daban daban domin samar da cigaba yadda ya kamata. Ya kuma jaddada cewa koyon Al adu daga Al ummomi daban daban zai takarawan gani wajen kare Al adu dama infanta rayuwar Al umma baki daya. Ya kuma kirayi membobin kungiyar da sukasance masu bin doka da oda a koda yaushe domin samar da inganceccen tsaro harma da cigaba. A jawabinsa uban kungiyar ta boys brigade a karamar hukumar ta Girei Mr Pngar Gwari ya baiyana irin muhimmancin da shirya irin wannan taro yakae dashi saboda yara zasu amfana da taron da kuma samun fahintar Al adu a bangarori daban daban. Ya shawarci mahalarta taron da suyi amfani da abinda sukaji domin samar da zaman lafiya hadin kai a tsakanin Al umma. Anashi bangaren shugaban kwamitin shirya taron Mr Goroson John ya godewa mahalarta taron da kuma baiayana rfarin cikinsa dangane mayan baki da suka samu damar halartar taron. An dai gudanar da rawai rawain gargajiya da Al adu daban daban da suka hada da Michika, Higi, da dai sauransu.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.