An shawarci malamai masu gabatar da nasihohi a wurin bukukuwar maulidi da su maida hankalin wajen hadin kan Al umma.

An kirayi malamai musammanma wadanda ke gabatar da nasihohi da jawabai a wurin bukukuwar maulidi da su maida hankali wajen fadakar da al umma musulmai dangane da hadin kai dama tarbiya a tsakanin al umma. Mallam Isma ila Modibbo Umar ne ya baiyana haka a zantawarsa da jaridar Al Nur Hausa a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Malam Isma ila Modibbo yace yana da muhimmanci malamai su maids hankali wajen baiyana halayen manzon Allah yadda ya zauna da kowa lafiya da kuma jan hankali jama a wajen yin karatu domin samun cigaban addinin musulunci. Malam Isma ila yace bikin maulidi yana da tarihi sosai saboda haka ana gudanar da bikinne domin tunawa da ranan haifuwar manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi. Tare kuma da gudanar da nasihohi daban daban dama baiyana tarihin manzon Allah. Malam Umar ya kuma kara da cewa akwai bukatar Al umma musulmai sukasance masuyin koyi da halayen manzon Allah. Wanda acewarsa hakan zaitaimaka wajen hadin kan al umma musulmai harma da samar da zaman lafiya mai daurewa a tsakanin al umma baki daya. Ya kuma shawarci Al umma musulmai da su maida hankali wajen yin adu o i domin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin kalubalen tsaro dake ciwa kasan nan tuwo a kwarya, da kuma wanzar da zaman lafiya a fadin Najeriya baki daya. Malamin ya kuma shawarci al umma musammanma mahalarta bukukuwar maulidi da sukasance suna amfani da abinda sukaji a wurin bikin na maulidi domin samun cigaban da Samar da hadin kai a tsakanin al umma musulmai.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.