An shawarci manoma da sukasance suna tuntuban malamain goma domin bunkasa harkokin noma.

An shawarci manoma da sukasance masu neman ilimin harkokin noma a koda yaushe domin samun damar gudanar da inganceccen noma harma da samar da wadaceccen abinci a fadin Najeriya baki daya. Alhaji Adamu Jnigi ne ya bada wannan shawara a zantawarsa da jaridar Al Nur Hausa a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Alhaji Adamu Jingi yace yanzu haka noma ya koma na zamani don haka akwai bukatar manoma su maida hankali wajen tuntubar malamai gona domin kaucewa da na sani. Kuma da zaran sunga abunda basu ganeba a gonakainsu da su gaggauta nemo malamain gona domin magance matsalar. Da yake amsa tabbaya dangane da mutane su shiga harkokin noma sai Alhaji Adamu yace yakamata Jama a su rungumi harkokin noma, domin a cewarsa Najeriya tana da sama da mutane milyon biyu kuma mutane kadanne suke noma. Don haka akwai bukatar karin jama a da su shiga a dama dasu a harkokin noma wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen samun saukin farashin kayakin noma. A yayinda ake kokarin girbe amfanin gona kuwa Alhaji Adamu ya kirayi manoma da sukasance masuyin taka tsantsan musammanma a bangaren ajiya wajen yin amfani da sanadiren adana kayakin abinci, domin kaucewa kamuwa da cututtuka. Da wannan nema yake shawarta manoma da su rinka tunttuba masana kafin suyi adanan kayakin abinci wanda hakan zai taimaka wajen samun cigaban Adana kayakin abinci yadda yakamata. Ya kuma kirayi gwamnatin tarayya dana jaha da sukasance suna taimakawa manoma musammanma kananan manoma dake yankunan karkara domin bunkasa harkokin noma harma da bunkasa dattalin arzikin jaha da kasa baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.