Gwamna Ahmadu Fintiri na jahar Adamawa ya sha alwashin bunkasa harkokin kwallon dawaki wato polo a fadin jahar.
Gwamnatin jahar Adamawa ta baiyana shirin ta na shiga ƙawance
da kungiyar wasan kwallon dawaki ta kasa domin bada karfin gwiwar shiga harkokin wasar a jahar.
Gwamnan jahar Adamawa,
Ahmadu Umaru Fintiri ne ya sanar da haka yayin bikin rufe gasar kwallon dawaki na 2023, wanda kungiyar ya shirya a birnin Yola fadar jahar.
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri yace gwamnatin jahar za ta ci gaba da tallafawa wasar a jahar domin cin gajiyar albarkatun da ke cikin ta.
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri wanda ya baiyana sha'awar shi a wasan yace wasan na kunshe da harkokin bude ido da na tattalin arziki, tare da karin cewa gwamnati zata tabbatar da kyakkyawar yanayi da zai kawo ci gaban wasan.
Gwamnan yace, kasancewar jahar Adamawa wata muhimmiyar matattarar na yankin arewa maso gabashin Najeriya, jahar na shirye domin shiga ƙawance dama tallafawa kungiyar wasan ƙwallon dawaki ta kasa domin tatsar duk wani alfanu dake tattare da wasan.
Yayin da ya ke jinjina wa bajintar yan wasan, Gwamnan ya yaba da kokarin mai martaba lamido Adamawa, Muhammadu Barkindo Aliyu Mustafa da irin tallafi da goyon baya da yake baiwa wasan ƙwallon dawaki a jahar.
Gwamna Fintiri yace ba za a iya misalta irin muhimmanci da wasan ke da shi ba , shi yasa ake bukatar cin moriyar shi a dukkan fannoni da ake da su.
Gwamnan ya kuma bada kyautan wadanda suka lashe kofin Gwamna a gasar Naira miliyan biyar, tare da alkawarin cewa daga badi za a fito da kofin mai martaba sarkin mubi a gasar kuma duk wanda suka yi nasara za su samu kyautar Naira miliyan uku.
A jawabin na maraba, kyaftin na kungiyar kwallon dawaki na Yola, Mohammed Baba ya baiyana farin cikin shi na cewa bayan dogon lokaci sakamakon cutar COVID-19, an kuma komo fafatawa.
Mohammed Baba ya jinjina wa mai martaba lamido Adamawa wanda shine uba kuma shugaban kungiyar na tsawon ran shi, Dakta Muhammadu Barkindo Aliyu Mustafa da irin na mijin kokarin da tallafi da yake bayar wa.
Wasan ƙwallon dawakin na yan wasa guda goma, biyar daga ko wane bangare an fara shi a Yola ne a shekara 1935 , a kofar gabashin fadar lamido, kafin a mayar da filin shi na yanzu.
Kuma wasu daga cikin wadanda suka fara bugawa a wancan lokaci sun haɗa da marigayi mai martaba lamido Adamawa Alhaji Aliyu Mustafa, da marigayi malam Umaru wambai, da marigayi malam Barade Hammawa da kuma marigayi Shettima Garga da dai sauransu.
Gasar na bana dai gwamnatin jahar Adamawa ce ke kan gaba gurin daukan nauyin ta, tare da wasu masu daukan nauyi kamar su majalissar masarautar jahar Adamawa , sai Alhaji Atiku Abubakar da Alhaji Abdulkadir Mamba, da Boss Mustafa, da Alhaji Modi Halilu da kuma comrade Salihu Mustafa da dai sauransu .
Comments
Post a Comment