Gwamnatin jahar Adamawa ta lashi takwabin inganta harkokin noma a fadin jahar.

Gwamnatin jahar Adamawa ta kudiri aniyar inganta harkokin noma dama samar da kasuwancin kayakin noma a fadin jahar baki daya. Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jahar Adamawa ne ya baiyana haka a lokacinda yake jawabi a wurin kaddamar da bada rance kasuwamcin kayakin noma karkashin shirin nan na Agribusiness. Wato Adamawa Agribusiness Support ADAS Programme.wanda ya gudana a gidan gwamnati dake nan yola.
Gwamna Fintiri yace shirin zaitaimakawa wadanda zasu amfana da tsarin ta samun damar basu rance daga Bankuna domin gudanar da harkokinsu yadda ya kamata. Gwamna ya kuma kirayi daukacin al umma jahar da sucigaba da hakuri biyo bayan hawhawan farashin kayakin abinci dama tsadar rayuwa da ake ciki da yardan Allah nan bada dadewaba komai zai koma daidai.
Ya kara da cewa gwamnatinsa zata cigaba da baiwa al umma tallafi domin rage musu radadin wahala da ake ciki a yanzu. Shima a jawabinsa sakataren gwamnatin jahar Adamawa Barista Auwal Tukur yace tsarin na ADAS zai samar da kudade ahiga sama da nera bilyon daya. An gabatarwa wadanda suka amfana da tsarin takardan shaidar samun rancen kudin. Taron ya samu halartan manyan Jami an gwamnatin jahar da suka hada da kwamishinoni, shugaban ma aikatan gidan gwamnati Dr Edgar Amos da dai sauraunsu. Akalla nera bilyon biyar ne dai aka ware domin tafiyar da shirin na harkokin kaauwanci kayakin noma a fadin jahar ta Adamawa. Wanda kuma hakan zaitaimaka wajen samar da aikinyi musammanma a tsakanin matasa dake fadin jahar.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.