Gwamnatin jahar Gombe ta dauki dawainiyar Kai daluben jahar zuwa jihohin da suke karatu karkashin Shirin misayan dalube.

kokarinta na magance matsin tattalin arziki da aka shiga sakamokon cire tallafin mai fetur gwamnatin jahar Gombe ta dauki dawainiyar kai daluben jahar dake karatu a makarantu daban daban dake fadin arewacin Najeriya. A cikin tsarin nan na musayar daluben. Da yake yiwa dalube jawabi kafin tashinsu zuwa jihohi da suke karatu darctan shirin na musayan dalube na ma aikatan ilimi a jahar Gombe Audu Garba ya shawarci daluben da sukasance masu nuna halaye na gari a duk inda suke karatu domin samun albarka da kuma cigaban ilimi da suka koya. Ana shirya tsarin musayan daluben ne domin samar da hadin kai a tsakanin daluben dake yankin na arewacin Najeriya. Audu Garba ya yabawa gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jahar Gombe bisa daukan dawainiyar kai daluben a jihohi daban daban dake yankin arewacin Najeriya. Darectan ya baiyana cewa an dauki matakin hakane domin sauwakawa iyayen daluben duba da irin yanayi da akeci na manatsanancin rayuwa. Shugaban kamfanin sifirin jahar Gombe wato Gombe Line Kwamuret Sani Sabo yace tuntunin aka horar da dukkanin direbobin da zasuyi jigilan daluben zuwa jihohin domin ganin anyi jigilansu lafiya ba tare da wata matsalaba. Shima yabawa yayiwa gwamnatin Muhammadu Inuwa Yahaya bisa kokarinsa na tabbatar da ganin daluben sun isa jihohin da suke karatu lafiya. Da take magana a madadin iyaye Fatima Bappa Yaya ta godewa gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa gudanar da kyakkawar shugabanci wanda kuma al umma na bukatan haka. Ta kuma kirayi daluben da sukasance jakadu na gari da kuma nuna kyawawan dabi u domin kare Martaban jahar ta Gombe.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.