Kamfanin Auwalus Business Concept ya dauki matasa aiki a wani mataki na rage rashin aikinyi a tsakanin matasa.
Kamfanin Auwakus Business Concept ya fara harar da ma aikata da ya dauka aiki domin ganin sun gudanar da aiyukansu yadda ya kamata ba tare da matsalaba.
Shugaban kamfanin Alhaji Auwal Usman ne ya baiyana haka a lokacinda ya jagorancin horar da ma aikata a kamfanin dake yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Alhaji Auwal yace sun dauki matakin horar da ma aikatanne domin sanin makaman aiki ganin cewa basu samu matsalar gudanar da aiyukansuba.
Ya kuma jaddada aniyarsa na ganin cewa matasa sun dogara da kansu wajen samun sana o i daban daban wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen inganta rayuwar matasan harma da samar da zaman lafiya a tsakanin jama a baki daya.
Da wannan nema yake shawartan matasa da kada suyi kasa a gwiwa wajen rungumar sana o i dogaro da kai domin kare nartabarsu dama cigaban al umma.
Kawo yanzu dai kamfanin ya debi ma aikata talatin kuma an rarrabasu rukuni rukuni wato rukunin A, rukunin B da kuma rukunin C domin samun damar horar dasu yadda ya kamata.
Wasu daga cikin matasan da suka zanta da manema labarai sun baiyana farin cikinsu dangane da daujansu aiki da kuma basu horo domin sanin makaman aiki. Tare da godewa kamfanin na Auwalus Business Concept bisa wannan na mjin kokari da yayi wajen daukansu aiki wanda kuma hakan abun a yabane.
Kuma suna fatan zauran kamfanoni zasuyi koyi da kamfanin na Auwalus wajen samarwa matasan aiki domin rage rashin aikinyi a tsakanin matasa dake ci musu tuwo a kwarya.
Comments
Post a Comment