Kotu sauraren kararrakin zabe gwamna ta tabbatarwa gwamnan jahar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya cewa shine halacceccen zaben gwamnan jahar Gombe.

Rahitanni daga jahar Gombe na cewa kotun sauraren koke koken kararrakin zabe tayi watsi da kaararakin da aka shigar mata na kalubalantar nasaran cin zaben gwamnan jahar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya da mataimakinsa Manasah Daniel Jatau. Kotun ta babbatarwa gwamnan cewa shine halalceccen gwamna a zaben gwamna da akayi a shekara ta dubu biyu da aahirin da uku a jahar ta Gombe. Kotun mai mutum uku karkashin jagorancin mai shariya S B Belgore tayi watsi da karanda yan takaran gwamna a karkashin jam iyar ADC Nafi u Bala dana jam iyar PDP Jibril Barde inda suke kalubalantar nasaran cin zabe da gwamna Inuwa Yahaya yayi da shi da mataimakinsa Manasah Daniel Jatau. A karanda jam iyar PDP ta shigar tare da dan takaranta inda suka zargi cewa an tafka magudi a zaben wanda hakan ya suka garzaya kotu domin bin kadun zaben. Itama anata bangaren Jam iyar ADC da dan takaranta suma kalubalantar zaben sukayi da cewa an tafka arangizon kuri u wanda hakan ya baiwa Inuwa Yahaya nasara don haka dolene su garzaya kotu domin neman hakkinsu. Da yake yanke hukunci mai shariya S B Belgore ya tabbatar da nasaran cin zaben gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da mataimakinsa Manasah Daniel Jatau, biyo bayan rashin kwararan hujjoji da jam iyun PDP dana ADC suka gaza gabatarwa kotun.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE