Kwamishinan Yan sanda jahar Adamawa ya rarraba kayakin tallafi.

Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya rarrabawa Jami an yan sanda kayakin tallafi wanda gwamnatin jahar Adamawa ta bayar. Hakan na kunshene a cikin wata sanarwa dauke da snaya hanun kakakin rundunan yan sanda jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje da ya fitar a yola.
Kwamishinan yan sandan ya karbi buhunan shinkafa dari da hamsin (150) an kuma rarrabawa marassa karfin dake cikin Jami an yan sandan, musammanma marayu wadanda iyayensu suka rasa rayukansu a lokacinda sukeyiwa kasa aiki.
Kwamishinan yan sandan ya godewa gwamnatin jahar Adamawa bisa kokarinta na cigaba da taimakawa rundunan yan sandan don haka rundunan zata cigaba da inganta tsaro domin kare rayuka dama dukiyoyin al umma jahar baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE