Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya fara horar da mata yan Jarida na kwanaki uku a jahar Taraba.

Daga Ibrahim Abubakar Jalingo
Ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya ya fara horar da mata yan Jarida na kwanaki uku a jahar Taraba domin inganta aiyukansu a zamunance ba tare da fargaba ba da Kuma bada rahoton da zai kawo cigaba a yankin arewa masau gabas.
Horan wanda ofishin jakadancin Amurka tare da hadin gwiwar kungiyar na Organization for Innovation anda Sustainable Development suka shirya a wani matakin na Samar da dai daito aikin Jarida ga mata a yakin na arewa masau gabashin Najeriya.
Yan Jarida mata a jahar Taraba dai na fuskantar kalubale da dama a duk lokacinda suke gudanar da aiyukansu a Arewacin Najeriya. Wani masana dai na cewa horon zai karwa matan kwarin gwiwar gudanar da aiyukansu bisa kwarewa domin ganin an samu nasaran cigaban dama wanzar da zaman lafiya a yankin na arewa masau gabas dama kasa baki Daya.
Sama da mata dari da hamsin ne dai ake saran zasu samu horon a yankin arewa masau gabas domin ganin mata su samu kwarewa wajen aikin Jarida. A cewa ofishin Jakadancin Amurka dake Najeriya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE