Rundunan yan sanda a jahar Adamawa ta cika hanu da wani da ake zargi da yiwa wata daluba fyade.
Rundunan yan sanda a jahar Adamawa tace tayi nasaran cafke Dan shekara ashirin da uku Mai suna Safiyanu Abubakar dake zaune a Unguwar chamber a cikin karamar hukumar Toungo a jahar Adamawa bisa zarginsa da yiwa wata daluba fyade.
Wanda ake zargin dai yayi anfani damar ne a yayinda ya ziyarci daluba inda yayi anfani da wani sanadari ta sanya mata a cikin abinsha domin ya gusar mata da hankali.
Wanda ake zargi ya tabbatar da aikata laifi inda yace yayi anfani da wannan damarne wajen sanya mata abinda zai gusar mata da hankali.
Tunin dai kwamishinan Yan sanda jahar Adamawa ya bada umurnin gudanar da bincike kan lamarin Kuma da zaran an kammala bincike za a gurfanar da Wanda ake zargin gaban kotu domin ya fuskanci shariya.
Comments
Post a Comment