Rundunan yan sanda a jahar Adamawa ta kama wani da ake zargi dayiwa yar shekaru fyade.

Rundunan yan sanda a jahar Adamawa tayi nasaran cafke wani da ake zargi da yiwa wata yarinya yar shekaru hudu da haifuwa fyade. Kakakin rundunan yan sandan a jahar Adamawa SP Suleiman Yahay Ngurojene ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yola. Sanarwan tace mutumin da ake zargi mai shekaru talatin da biyu da haifuwa wato Mika Bitrus wanda yake zaune a Garin Sangere kan titin zuwa Girei wanda kuma ana zarginsa da yuwa wata yarinya mai shekaru hudu da haifuwa fyade. An dai samu nasaran damke mutuminne biyo bayan karafi da uwar yarinyar Fatsuma Abdullahi da shigar a ofishin yan sanda dake Girei, wanda kuma hakan yasa rundunan yan sandan batayi kasa agwiwaba wajen gudanar da bincike akan lamarin. Bincike da aka gudanar ya baiyana cewa shi wanda ake zargin dai masana ar kafintane kuma ya aikata laifinne ga yar makwabcinsa. Tunin dai kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya bada umurnin gudanar da bincike dangane da lamarin kuma da zaran an kammala bincike za a gurfanar da wanda ake zargin gaban kotu domin ya fuskaci shariya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE