Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta lashi takwabin Saka kafar wando Daya da duk Wanda yayiwa doka Karen tsaye a lokaci dama bayan bukukuwar Maulidi.

Rudunan yan sandan jahar Adamawa tare da sauran hukumomim tsaro sun kimtsa tsaf domin ganin an gudanar da bukukuwar Maulidi lafaiya ba tare da matsalaba. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a yola wanda aka rarrabawa manema labarai. Sanarwa na mai gargadin cewa rundunan zata saka kafarwando daya ga duk wanda ke barazanar karya doka ko kuma ko kuma yiwa zaman lafiya barazana. Don haka jama a su kaucewa duk abinda zai kawo tashin hankali a lokaci dama bayan bukukuwar bikin na Maulidi a fadin jahar. Sanarwan ta cigaba da cewa Al umma musulmai su tafi zuwa wuraren da za a gudanar da bukukuwar lafiya ba tare da fargababa domin rundunan yan sandan ta dauki dukkanin matakai da suka dace domin kare rayuka dama dukiyoyin Jama a. Sanarwa ta kirayi daukacin al umma da su baiwa hukumomin tsaro hadin kai da goyon baya da kuma kai rahoton dukkanin abinda basu amince dasuba zuwa ofishin yan sanda mafi kusa. Domin daukan mataki gaggawa akai.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE