Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta tarwatsa tare kama wadanda ake zargi dayin garkuwa da mutane domin Neman kudin fansa.

kokarinta na inganta tsaro da Kuma jaddada aniyarta na dakile aiyukan ta addanci a tsakanin Al umma. Rundunan yan sandan jahar Adamawa tare da hadin gwiwar mafarauta da kungiyar miyetti Allah sun dakile aiyukan masu garkuwa da mutane da suka addabi yankin Tambo a karamar hukumar Girei a jahar Adamawa. Kawo yanzu dai Rundunan yan sandan na tsare da mutane bakwai wadanda ake zargi da aikata laifuka garkuwa da mutane a yankin na Tambo. An samu nasaran cika hanu da mutane biyo bayan samun bayanain sirri da Kuma dabaru da aka dauka Wanda hakan yasa suka yarwatsa wadanda ake zargi daga maboyarsu biyo bayan garkuwa da sukayi da wani Mai suna Koire Alhaji Ruwa inda suka bukaci kudin fansa da yakai nera milyon goma. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a yola. Sanarwa ta baiyana cewa kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya baiyana farin cikinsa dangane da wannan nasara da akayi Kuma ya bada umurnin daukan dukkanin matakai da suka dace domin dakile aiyukan masu garkuwa da mutane. Kwamishinan ya Kuma kirayi daukacin Al ummar jahar Adamawa da akoda yaushe sukasance suna taimakawa rundunan da duk wasu bayanain sirri da zaibaiwa rundunan damar dakile aiyukan bata gari a tsakanin Al umma.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE