Rundunan yan sandan jahar Adamawa tana tsare da wani matashi da ake zargi da kisan Kai.

A yanzu haka rundunan rundunan yan sandan jahar Adamawa tana tsare da wani mataahi mai suna Zakaryau Sa ad dan shekarau 19 da haifuwa wanda ke zaune a Anguwar Wuro Hausa dake cikin karamar hukumar Yola ta Kudu dake jahar Adamawa bisa zarginsa da kashe wani matashi mai suna Muhammed Yahaya. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da rabawa manema labarai a yola. Kama wanda ake zargin biyo bayan rahoton da mazauna Anguwar Damdu a karamar hukumar yola ta kudu suka kai ofishin yan sanda cewa gawani da basusan ko wayeba kwance a cikin jin biyo bayan jimasa da akayi a wuya. Nan dana DPO ofishin yan sandan dake yola ya garzaya dashi zuwa asibitin daga bisani ya mutu. Tunin kwamishina yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya umurci mataimakin kwamishinan yan sanda dake kula da sashin binciken manyan laifuka wato CID da yacigaba da gudanar bincike dangane da lamarin kuma da zaran an kammal bincike za a gurfanar dashi gaban kotu domin ya fuskaci shariya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE