Rundunan yan sandan jahar Adamawa yanzu haka tana tsare da wani Wanda ake zargi dayiwa matar makwabcinsa fyade

yan sandan a jahar Adamawa tayi nasaran cafke wani dan shekaru talatin da shida da haihuwa wanda ke zaune a Anguwar Diocese a Kala a dake cikin karamar hukumar Hong bisa zarginsa dayiwa matar bakabcinsa yar shekara ashirin da daya fyade. Jami in hulda da jama a na rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar wanda aka rabawa manema labarai a yola. Sanarwan tace mutumin mai suna Jafar Adamu ya samu nasaran yin hakane bayan ya fahinci makabcin nasa baya gida ya tafi gona saboda haka ya kutsa cikin gidan tare da tilasawa matar makabcin nasa da ta amince da bukatar tashi ko kuma ya jimata. Bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya shiga gidanne fuskarsa a rufe dauke da wuka inda ya tilasta mata da ta yarda da bukatarsa, sai akayu rashin sa a yana cikin aikata laifin sai abinda yasa a fuskarsa ya fadi dagan ne fa yayi tsalle da taga ya fita da gudu.
Bayan aukuwar lamarin sai mijin matar ya kai kara ofishin yan sanda dake karamar hukumar ta Hong a jahar Adamawa. Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola yayi tir da wannan lamarin don haka nema ya bada umurnin mika lamarin ga sashin laifukan iyali domin cigaba da bincike kuma da zaran an kammala bincike za a gurfanar dashi gaban kotu domin ya fuskanci shariya. Kwamishinan ya kuma kirayi daukacin al umma jahar Adamawa da sukasance suna taimakawa rundunan a kokarinta na yaki da aikata laifuka a fadin jahar baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE