Rundunan yan sandan Najeriya zata gudanarwar karnuka Alura riga kafi kyauta a fadin Najeriya
A yayinda aka gudanar da bikin ranan cizon Kare na duniya rundunan yan sandan Najeriya ta ta kudiri aniyar yiwa karnuka aluran riga kafi domin rage kaifin guba a wani mataki na inganta kiwon lafiya a tsakanin al umma.
Kakakin rundunan ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya baiyana haka a wata sanarwa ya fita aka rabawa manema labarai a Abuja.
A sanarwan anjiyo Babban sifeton yan sandan Najeriya Kayode Adeolu Egbetokun na cewa bikin ranan cizon kare karo na sha bakwai mai taken lafiya ga kowa don haka rundunan ta dauki dawainiyar yiwa karnuka aluran Riga kafi kyauta, a duk fadin Najeriya. A wani mataki na kawar da cutar dake sahafa mutane dama dabbobi.
Don haka rundunan yan sandan a Najeriya taga ya dace ta dauki matakin magance matsalar na cizon karnuka a tsakanin al umma , don haka daga yau 28-9-2023 za a fara aluran Riga kafin a dukkanin karnuka a dukkani cibiyoyin kula da lafiyar dabbobi na rundunan dake fadin kasan nan.
A cewar Babban sifeton yan sandan dai rundunan yan sandan zata taka rawan gani domin ganin an gudanar da Riga kafin yadda ya kamata wanda za a dauki tsawon wata daya anayi, domin kare al umma daga cututtuka da ake samu sakamokon cizon karnuka.
Babban sifeton yace rundunan a karkaahin ahugabancinsa zaiyi sukkanin maiyiwa domin ganin an samu cigaban kiwon lafiya. Da wannan nema yake kiran yan Najeriya da su baiwa rundunan hadin kai da goyon baya domin ganin ta cimma burinta na magance matsalar baki daya.
Ranan 28-9- ma kowace shekara ne ake gudanar da biki na ranan cizon karnuka domin dubawa tare da neman hanyar magance matsalar baki daya.
Comments
Post a Comment