Tashin bom yayi sanadiyar kashe mutane 50 a Pakistan.

.
Akalla mutane hamsin suka mutu wasu hamsin kuma suka jikkata sakamokon harin kunan bakin wake da aka kai a wurin bikin Maulidi a Pakistan kamar yadda hukumar Yan sandan kasar ta baiyana. Lamarin dai ya farune a kusa da masallaci dake arewa masau yamma na lardin Balochistan a dai dai lokacinda ake gudanar da bikin Maulidi tunawa da ranan haifuwar mazon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi. Yanzu haka dai hukumomi a lardin na Balochistan sun aiyana dokan ta baci domin maida da zaman lafiya a yankin. Kawo yanzu dai ba wata kungiya da ta dauki nauyin Kai harin. An sake samun tashin wani bom a masallaci dake kusa da birnin Peshawar a Khyber dake lardin Pakhtunkhwa. Sai dai har yazuwa yanzu ba Akai ga gano wadanda suka jikkata ko rasa ratukaba. Duk da cewa bom din yayi sanadiyar lalata gine ginen masallacin.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE