An buiaci mata su maida hankali wajen baiwa yara tarbiya..

An kirayi mata musulmai da sukasance masu Neman ilimin addinin musulunci da Kuma tura yaransu makarantu domin su samu ilimin addinin dana zamani Wanda acewarta hakan zai taimaka wajen samun yara na gari dama ingancaccen tarbiya a tsakanin yara. Amiran kungiyar mata musulmai ta tarayya wato FOMWAN Shiyar jahar Adamawa Khadija Buba ce tayi wannan kira a zantawarta da manema labarai Jin kadan da kammala taron Da awa da aka gudanar a Victim dake cikin karamar hukumar a jahar Adamawa. Malama Khadija tace Neman ilimi wajibine ne ga Al umma musulmai don haka Yana da muhimmanci Al umma musulmai su dukufa wajen Neman ilimi tare Kuma da tura yaransu makarantu domin su samu nagarceccen ilimi sukasancewa sune shuwagabanin gone. Ta Kuma shawarci shuwagabanin dama malamai da su tashi tsaye wajen fadakar da Al umma mahimmancin zaman lafiya da hadin Kai a tsakanin Al umma. Wanda acewarta hakan zai kawo cigaba dama zaman lafiya Mai daurewa. Harwa yau da kirayi Yan Najeriya da sucigaba da yiwa kasa adu o I domin Neman taimakon Allah Madaukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin kalubalen tsaro a fadin Najeriya baki Daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE