An bukaci gwamnati jahar Adamawa da maida hankali wajen mata dake dauke da cutar yoyon Fitsari a fadin jahar.

kirayi gwamnatin jahar Adamawa tare da masu ruwa da tsaki da sukasance suna yin jinyan mata dake dauke da cutar yoyon fitsari domin cetosu daga kincin rayuwa da suke ciki bayan sun kamu da cutar. Shugaban Gidauniyar Fistula a Najeriya Mallam Isa Musa ne yayi wannan kira a lokacinda yake jawabi a wurin karkare horo da akayiwa mata da suka warke daga cutar yoyon fitsari bayan an musu fidar cutar. Horon dai ya gudanane karkashin jagorancin Gidauniyar Fistula tare da hadin gwiwar UNFPA da UNFCU da Kuma ma aikatar harkokin mata ta jahar Adamawa Wanda aka gudanar a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Mallam Isa Musa yace Gidauniyar ta fistula tayi jinyar mata wadanda ke dauke da cutar yoyon fitsari a sassa daban daban dake fadin kasan man. Mallam Isa yace a yanzu haka Gidauniyar ta horas da mata da suka warke daga cutar yoyon fitsari akalla hamsin a jahar ta Adamawa kan Sana o I daban daban da suka hada da aikin tela, injin Nika, yin sabulu da dai sauransu. Ya Kuma tabbatar da cewa zasu cigaba dayin irin wadannan aiyuka har sai an samu saukin cutar a tsakanin mata tare da Kiran iyaye dama mazajen matan da suka samu laruran cutar ta yoyon fitsari da kada su kyamacesu sukasance masu lura da su saboda cutace da ake warkewa. Anata bangaren Babar sakatariya a ma aikatar harkokin mata a jahar Adamawa mis Rifkatu Gwandi Wanda Darekta a ma aikatar Edward Yadzigwa ya wakilta godiya yayiwa Gidauniyar ta fistula bisa wannan namijin kokari da sukayi na haras da matan a jahar Adamawa. Tare da shawartan wadanda suka samu horon da suyi amfani da abinda suka samu yadda ya kamata domin su dogara da kansu, Wanda acewarsa hakan zaitaimaka musu wajen rage radadin wahala da suke ciki. Anata jawabi Barista Fatima Raji ta kirayi Al umma musammanma sarakunan gargajiya da sukasance masu sanya ido a Koda yaushe domin ganin an samu saukin cinzarafin yara kanana a tsakanin Al ummah. Wasu daga cikin wadanda suka amfana sun baiyana godiyarsu da Jin dadinsa dangane da wannan horo da suka samu don hakanema suke godewa Gidauniyar ta fistula tare da abokan huldarsu bisa wannan taimako da suka yi musu Kuma sunyi alkawarin maida hankali kan abinda aka koya musu domin ganin sun samu nasaran bunkasa kasuwancinsu. Taron dai ya samu halartan manyan ma aikatan gwamnatin jahar Adamawa, masu ruwa da tsaki harma da sarakunan gargajiya da dai sauransu.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE