An bukaci mabiya addinin kirista da suyi amfani da wannan lokaci wajen yin adu o I zaman lafiya..

Gidauniyar Attarahum a jahar Adamawa tana Mai taya mabiya addinin kirista bikin kirsimeti dafatan za ayi bikin lafiya. Shugaban Gidauniyar ta Attarahum na jahar Adamawa Mallam Mukhtar Dayyib ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Bayan taya murnan sanarwan ta Kuma kirayi mabiya addinin kirista da suyi amfani da wannan lokaci wajen yiwa jaha dama kasa adu o I Samar da zaman lafiya dama neman taimakon Allah Madaukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin kalubalen tsaro a fadin Najeriya baki Daya. Sanarwan ta Kuma kirayi jama a da sukasance suna taimakawa hukumomin tsaro da wasu bayanai da zai taimaka wajen dakile aikata laifuka a tsakanin Al umma. Da wannan nema ake kira ga iyaye da su maida hankalin kan yaransu domin ganin ba a samu wata matsalaba a lokaci dama bayan bikin na kirsimeti.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE