An bukaci shuwagabanin da sukasance masuyin adalci a dukkanin aiyukansu.

An kirayi shuwagabannin da sukasance masu gudanar da shugabanci bilhakki da gaskiya da adalci domin samun tsira ranan gobe kiyama. Dr Bashir Imam Hong ne yayi wannan kira a lokacinda yake gabatar da makala a wurin kammala bitan dangane da kyakkawar shugabanci na kwana biyu Wanda majalisar Addinin musulunci na karamar hukumar yola ta kudu ta shirya a yola Dr Bashir yace shuwagabanin su sanifa akwai hakkik wadanda suke mulka Kuma za a tambayesu ranan gobe kiyama dangane da yadda suka gudanar da shugabanci. Ya Kuma kirayi Al umma da sukasance masu yiwa shuwagabanin biyayya da adu o I domin ganin an samu zaman lafiya da cigaba. A jawabinsa shugaban taron Barista Bello Hamman Diram yace shirya irin wannan bitan Yana da muhimmanci domin hakan zaitaimaka wajen sanin makaman shugabanci dama gudanar da kyakkawar shugabanci Wanda acewarsa hakan zaitaimaka wajen Samar da zaman lafiya Mai daurewa. Muhammed Bashir Buba Wanda shinema shugaban majalisar Addinin musulunci a karamar hukumar yola ta kudu ya yabawa kokarinda majalisar a matakin jaha keyi na inganta makaman shugabanci . Ya Kuma baiyana gamsuwarsa da Jin dadinsa dangane da shirya wannan bita domin shuwagabannin zasu San makaman aiki da ilimantarwa dama sanin nauyin dake kansu. Wasu daga cikin wadanda akayi musu bitan sun baiyana farin cikinsu dangane da wanna bita da akayi musu Wanda acewarsu hakan zai basu damar sauke nauyi dake kansu.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.