An horar da mutane da zasu taimaka wajen kare cin zarafin jinci a jahar Adamawa.
Daga Ibrahim Abubakar Yola.
A wani mataki na inganta sashin shariya da Kuma magance matsalar da ake samu na banbancin jinci an horar da matasa akalla talatin a cikin karamar hukumar yola ta arewa da zasu taimaka wajen dakile matsalar.
Kungiyar lauyoyi mata a Najeriya wato FIDA tare da hadin gwiwar care international ne suka horar da matasa kamar yadda shugaban kare cin zarafin jinci Aisha Umar ya baiyana a tattaunawarta da manema labarai a Yola.
Tace horon ya gudanane karkashin HARP da FCDO Wanda Kuma an dauki kwanaki biyu ana gudanar da horon Kuma an dauki matakin hakanne domin ganin wadanda aka horardin suna da rawa da zasu iya takawa wajen magance matsalar cin zarafin jinci.
Don haka akwai bukatar wayarwa Al umma Kai dangane da kawo ga karshen matsalar baki Daya.
Aisha ta Kara da cewa wadanda aka horar din Suma suna da muhimmiyar gudumawa da zasu iya bayarwa wajen dakile matsalar baki Daya.
Da take gabatar da kasida wakiliyar kungiyar lauyoyi wato FIDA Aishatu Hamidun tace Yana daga cikin aiyukan Waanda aka horar din tabbatar da ganin an samu kyakkawar halaka a tsakanin Al ummah.
Itama anata jawabi Barista Fatima Aliyu Babakano tace duk da yanayi da ake ciki yin haka zai taimaka wajen rage jinkiri da ake samu wajen yanke shariya.
Da take nata jawabi Barista Fatima Raji ta kirayi Al umma da sukasance suna baiwa wadanda aka horardin goyon baya domin ganin an samu nasara magance matsalar baki Daya.
Mutane talatin din da aka horar din dai sun fitone daga angwannin da suka hada da Jambutu, Yelwa, Limawa, Damilu, da Kuma Nasarawo dukkaninsu suna cikin karamar hukumar yola ta arewa fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Comments
Post a Comment