An kirayi gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da ya Kara Gina rukunin gidajen gwamnati a fadin jaha.
Daga Ibrahim Abubakar yola.
da Makamain makarantu Dari ne dai wadanda sukayi ritaya a jahar Adamawa sun kirayi gwamnati karkashi jagoranci gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da da ya shiga tsakanin dangane da yi musu ba daidaina Wanda kwamitin cika aiki da gwamnan ya kafa kan gidajen gwamnati dake fadin jahar.
Malamain da lamarin ya shafa dai sun baiyana hakane a ganawarsu da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa, tsoffin malamain sun koka dangane da karancin wa adi da aka basu na da Subaru gidajen gwamnati lamarinda bai musu dadina da su da iyalensu saboda haka akwai bukatar gwamnati da ta shiga tsakanin tare kuma da inganta kudin sallama domin hakan zai basu damar Gina gidajensu.
Malamain karkashin shuwagabaninsu wato Monday Dickson da Salihu Buba Wokemso dukkanin sun baiyana cewa ba wani malami da ya amfana da rukunin gidajen gwamnati tunda tsohon gwamna Boni Haruna ya Samar.
Saboda haka suna kira ga gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da ya Kara Gina rukunin gidajen gwamnati musammanma a yankunan karkara domin malamai suma su samu sukuni domin Samar da zaman lafiya dama hadinkai
A cewarsu dai kwamitin karkashin jagorancin John Vandu a kwanan nan ne dai suka baiwa Wanda ke zaune a gidajen gwamnatin makarantu da ake kwana waadin fita daga gidajen a fadin jaha.
Comments
Post a Comment