An kirayi maniyata aikin Hajjin shekara ta 2024 da su gaggauta biyan kudadensu kafin ran 31-12-2023.
An kirayi maniyata zuwa aikin Hajjin shekara ta 2024 da su gaggauta biyan kudadensu kafin ran 31-12-2023 kamar yadda hukumar aikin Hajjin Najeriya NAHCON ta aiyana.
Ko odinata kungiyar Arewa New Egenda Sa Idu Bobbai ne yayi wannan kira a lokacin da yake jawabi a wurin wani taron wayar da Kai dangane da aikin Hajjin Wanda kungiyar ta Arewa New Egenda tare da hadin gwiwar majalisar Addinin musulunci na jahar Adamawa suka shirya a yola.
Sa Idu Bobboi yace ya kamata maniyatan sukasance sun kammala biyan kudaden nasu domin hakan me zai baiwa hukumar damar gudanar da aiyukan ta yadda ya kamata domin ganin an samu nasaran aikin Hajjin shekara ta 2024 lafiya na tare da wasu matsalaba.
Bobboi ya Kuma nuna takaicinsa dangane da har ya zuwa yanzu naiwuce Kaso 13 ne kawai suka biya kudadensu ba don wannan abun damuwane saboda haka ya kamata maniyatan su gaggauta biyan kudaden nasu.
Shima a jawabinsa shugaban majalisar Addinin musulunci a jahar Adamawa Mallam Gambo Jika ya kirayi maniyatan da sukasance masu maida hankalin wajen biyan kudaden nasu domin ganin an samu nasaran gudanar da aikin Hajjin lafiya.
Da yake nashi jawabi Babban sakataren hukumar Jin dadin Alhazain jahar Adamawa Mallam Salihu Abubakar Wanda Adamu Ahmed ya wakilta yace suna aiki ba dare ba rana domin ganin an Kai ga nasara saboda kasar Saudiya tace tana son ganin an kammala dukkanin shirye shirye aikin Hajji akan lokaci.
Da yake jawabi a madadin Jami an tsare tsaren aiki Hajjin kananan hukumomi a jahar Adamawa Alhaji Ya u Gambo ya kirayi hukumar aikin Hajji ta kasa da ta Sanar da kudin aikin Hajjin na shekara ta 2024 Wanda acewarsa hakan zai baiwa maniyatan damar biyan kudadensu yadda ya kamata.
Tun da farko dai hukumar aikin Hajji ta kasa wato NAHCON ta Sanar da cewa maniyaci zai ajiye kudi Milyon hudu da dubu Dari biyar kafin a sanar da kudin aikin Hajji na shekara ta 2024.
Comments
Post a Comment