An shawarci Yan Najeriya da sukasance masu riko da Al adunsu.

kirayi yan Najeriya da sukasance masu bunkasa Al adunsu a Koda yaushe domin samun cigaba hadin Kai harma da bunkasa tattalin Arzikin kasa baki Daya Shugaban cibiyar bunkasa Al adu da wayar da Kai wato NICO na kasa Ado Muhammed Yahuza ne yayi wannan kira a lokacinda yake jawabi a wurin wani bikin Al adu da cibiyar ta shirya a yola. Ado Muhammed Wanda daraktar cibiyar a shiyar arewa masau gabas Jen Anigela ta wakilta yace dalilin shiyar wannan biki dai shine wayawa Al umma Kai dangane da muhimmancin Al adu da Kuma irin gudanawa da Al adu ke bayarwa wajen hadin Kai dama zaman lafiya a tsakanin Al umma baki Daya. Ya Kuma kirayi matasa da su maida hankali wajen kula da Al adunsu a duk inda suke domin habaka Al adu wani mataki na magance bacewar Al adu a tsakanin Yan Najeriya. Ya Kuma kirayi gwamnati dama masu ruwa da tsaki da sukasance masu karawa Al umma kwarin gwiwar bunkasa Al adu domin Samar da cigaba yadda ya kamata. Shima anashi jawabi shugaban taron Musa Sa Idu ya godewa Nico bisa shrya wannan biki Wanda acewarsa hakan zai taimaka wajen cigaban Al adu a tsakanin dalube dake makarantu a fadin kasan. Ya shawarci dalube musammanma wadanda suka halarci bikin da suyi amfani da abinda aka fada musu na Al adu domin bunkasa Al adu yadda ya kamata. Abinda ya wakana a wurin bikin dai sun hada da gasar rawai rawain gargajiya. Muhawarori, da dai sauransu. Tare da bada kaututtuka ga wadanda sukayi zarra a gasar. Akalla makarantu gaba da firamare bakwai ne suka halarci bikin da suka hada da G D S S Doubeli, G D S S Viniklang, G D S S Capital School, G M M C, Aliyu Mustapha College, G G S S Yola, da Kuma Air force Comprehensive School.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE