Wata matashiya tayi Kunan bakin wake a jahar Adamawa.

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta samu rahoton cewa wata matashiya yar shekaru 22 da haifuwa Mai Suna Florence Vandi ya hallaka kanta biyo bayan Shan maganin kashe kwari wato otafiyafiya. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola. Ita dai marigayiya Florence yar karamar hukumar Munchikace Kuna tana zaune a Viniklang dake cikin karamar hukumar Girei a jahar Adamawa.ta Kuma Yi sanadiyar hallaka kantane biyo bayan damuwa da tayi sakamokon mutuwar saurayinta. Kuma ta dauki mataki hakanne Sa o I kadan bayan rasuwar saurayin nata Mai Suna Nuhu Boniface Wanda ya mutu sakamokon gajeriwar rashin lafiya da yayi fama da ita. Bin cike ya nuna cewa kafin rasuwar Florence ma aikaciyace a hukumar kiwon lafiya a matakin farko dake karamar hukumar Girei. Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya baiyana damuwarsa dangane da aukuwar lamarin don haka nema ya shawarci Al umma da su daina daukan doka a hanunsu da zaran sunga abunda bai kamataba su Kai rahoto zuwa ofishin Yan sanda mafi kusa.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE