Gidauniyar Attarahum ta jajantawa gwamnatin jahar Kaduna biyo bayan harin bom da ya hallaka mutane a karamar hukumar Igabi dake jahar Kaduna.
kirayi gwamnatin tarayya Dana jahar Kaduna harma da Yan majalisun dokoki na kasa da suyi dukkanin maiyiwa domin ganin anyiwa wadanda harin bom ya shafa a karamar hukumar Igabi dake jahar Kaduna.
Shugaban Gidauniyar Attarahum a jahar Adamawa Mallam Mukhtar Dayyib ne yayi wannan kira a zantawarsa da manema labarai a Yola.
Mallam Mukhtar yace ya zama wajibi a kirayi gwamnatin tarayya Dana jahar domin sune uwa danganr da lamarin saboda haka ya kamata akafa kwamitin da zai gudanar da kwararan bincike domin gano dalilin Kai wannan hari da Kuma hukunta duk wadanda aka samu da hanu a cikin Kai harin.
Gidauniyar ta Attarahum ta Kuma jajantawa gwamnatin jahar ta Kaduna dama iyalen dukkanin wadanda suka rasa yan uwansu tare da yi musu Adu ar Allah madaukakin sarki ya jikansu ya gafarta musu, wadanda suka jikkata Kuma Allah ya basu lafiya.
Ya Kuma kirayi hukumomin tsaro da sukasance masuyin taka tsan tsan a duk lokacinda suke gudanar da aiyukansu domin acewarsa irin wadannan lamari ya Sha faruwa ba a daukan kwarararar matakai Akai.
Mallam Mukhtar Dayyib ya shawarci Yan Najeriya da sucigaba da yin adu a domin ganin an kawo karshen matsalar tsaro a fadin Najeriya baki Daya.
Comments
Post a Comment