Gidauniyar Attarahum ta rarrabawa manoma taki a jahar Adamawa.

Attarahum ta rarrabawa marassa galihu taki da barguna domin inganta harkokin noma a wani mataki na Samar da wadaceccen abinci a fadin jahar baki Daya. Da yake rarraba kayakin shugaban Gidauniyar ta Attarahum a jahar Adamawa Mallam Mukhtar Dayyib yace sun samu wannan kayakinne daga Aishatu Dahiru Ahmed Binani Wanda ta taimakawa Gidauniyar da kayakin. Saboda haka nema Gidauniyar itama taga ya dace a taimakawa Al umma. Saboda haka suna fatan wadanda suka samu wadannan kayaki zasuyi amfani dasu yadda ya kamata tare da shawartansu da sukasance suna yiwa Aishatu Binani Ad uar ganin ta samu nasara dukkanin abinda take bukata Wanda acewarsa hakan zai bata damar cigaba da taimakawa Al umma da yakeyi. Ya Kuma kirayi daukacin Al umma da sucigaba dayiwa jaha dama kasa adu o I domin Samar da zaman lafiya Mai daurewa a kasa baki Daya. Shima anashi jawabi Mallam Abnas Abubakar Wanda Kuma shine ma anin Gidauniyar ta Attarahum ya baiyana cewa sun tarune domin rarraba kayakin domin baiwa mutane damar samun saukin rayuwa a tsakanin Al umma. Ya Kuma ja hankalin jama a da sukasance masu maida hankali wajen gudanar da aiyukansu yadda ya kamata ba tare da wasu matsaloliba Wanda hakan nema yasa suka rarraba wannan kayaki. Wasu daga cikin wadanda suka samu wannan taimako sun nuna farin cikinsu dangane da wannan taimako da Gidauniyar Attarahum tayi musu Wanda a cewarsu wannan taimako ya rage musu raddadin wahala da suke ciki. Tare Kuma dayiwa Aishatu Binani fatan Alheri Allah ya bata Sa a dukkanin abinda take nema. Kayakin da aka rarraba dai sun hada taki buhu hamsin Mai nauyin kg 50 da barguna kwaya 50.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE