Gidauniyar Attarahum ta taimaka da feshinaganin sauro a karamar hukumar yola ta kudu a jahar Adamawa.

Gidauniyar Attarahum shiyar karamar hukumar yola ta kudu dake jahar Adamawa ta gabatar da feshin maganin sauro a anguwar Mali dake karkashin Adarawo ward a wani mataki na kakabe cutar maleriya a tsakanin Al umma. Shugaban Gidauniyar ta Attarahum dake karamar hukumar yola ta kudu Malam Mahmud Umar Dikko ne ya jagoranci feshin maganin sauro Wanda akayi a kan juji dama magudanen ruwa dake yankin baki Daya. Malam Mahmud Umar yace sun dauki matakin hakane duba da yadda sauro ke addabar jama a Wanda Kuma hakan yasa ake yawaitar samun cutar maleriya, saboda haka suka ga hakan ya dace su taimaka da feshin domin jama a su samu lafiya da Kuma dakile cutar ta maleriya. Mallam Mahmud ya Kuma kirayi mazauna anguwar da sukasance masu tsafcace muhallensu a Koda yaushe domin kaucewa cizin sauro. Ya Kuma kirayi Al umma dake fadin jahar Adamawa da sukasance suna baiwa Gidauniyar ta Attarahum hadin Kai da goyon baya domin ganin ta cimma burinta na inganta rayuwar Al umma dake fadin jahar ta Adamawa. Wasu daga cikin mazauna anguwar sun baiyana farin cikinsu dangane da wannan aikin feshi da Gidauniyar Attarahum tayi musu, a cewarsu hakan zaitaimaka wajen rage matsalar sauro a anguwar baki Daya. Da wannan nema suke kira ga sauran kungiyoyi da suyi koyi da taimakon da Gidauniyar Attarahum keyi domin Samar da wadaceccen kiwon lafiya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE