Gwamnatin jahar Adamawa Tasha alwashin Samar da tsafcaceccen ruwa da ma hada Kai da hukumar shige da fishe.

Gwamnan jahar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya kara jaddada anniyar gwamnatin shi na samar da tsaftacacciyar ruwa mai kyau ga al’ummar jahar, Gwamna Ahamadu Umaru Fintiri ya kara jaddada anniyar gwamnatin nashi ne yayin rattaba hannu kan tsarin samar da albarkatun ruwa da na tsarin samar da ruwa da tsaftacciyar muhalli wato WASH, wanda aka daidaita. Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri yace ruwa na da muhimmanci matuka alafiyar bil’adama, tattalin arziki da ma sauran su, hakan ya sa rattaba wa wannan tsari na WASH hannu. Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri yace gwamnatin shi ta saka kudade da dama a sashin ruwa wanda haka ya kara bada tabbacin samar da ruwa, tare da Karin cewa da wannan rattaba hannu kan wannan tsarin, zai kara baiwa gwamnati karfin gwiwar saka wasu karin kudade a sashin. Gwamnan yace hakan zai taimaka matuka gurin Karin kudin shiga a sa shin harkokin ruwa, dama bada lasisi, da izini wa masu hakar ruwa da dai sauran su, tare da baiwa takwarorin gwamnatin tabbacin cewa zata kiyaye dukkanin dokoki dake kunshe a cikin wannan sabon tsari da aka rattaba wa hannu. Da yayi jawbi kan sabon tsarin, komishin albarkattun ruwa na jahar Adamawa, Mallam Ayuba Audu yace wannan rattaba hannu kan sabon tsarin, na kunshe cikin alkawurra da gwamnanti da dauka wa al’ummar jahar. Ya kuma godewa dukkan kungiyoyin kawancen ci gaba da ma’aikatun gwamnati da su taimaka gurin sake daidaita wannan tsari, da kuma hade shi a guri guda. Kungiyoyin kawancen ci gaban da suka taimaka gurin cin ma wannan nasara su hada da IRC, Goal Prime, Ciscope, Usaid WASH, Mercy Corp and water aid da dai sauran su.
Gwamnan Ahmadu Umaru Fintiri na jahar Adamawa y ace gwamnatin shi zata ci gaba da taimakawa hukumar shige da fice ta kasa gurin aiwatar da aiyukan ta na ci gaba da kare iyakokin kasa. Gwamnan ya baiyana haka ne yayin da ya karbi bakoncin sabon kontrollan hukumar da aka turo jahar Adamawa, Muhammadu Adamu wanda ya jagoranci wasu jami’an hukumar da suka kawo wa gwamnan ziyara a gidan gwamnati dake yola. Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri yace akwai kalubale da ake fama da su dangane da tsaron iyakoki a jahar ganin tana da kananan hukumomi tare dake da iyakoki da dama da suka hada jahar da wasu kasashe makwabta. Gwamnan yace, gwamnati zata dubi wadannan kalubale ta kuma ga abun da zata yi domin shawo kansu sabili da jami’an hukumar shige da ficen su gudanar da aiyukan su cikin sauki. Ya kirayi kontrollan da ya yi aiki da kwarewar shi gurin ganin hukumar ta yi iya kokarin ta domin ci gaban jahar dama kasa baki daya. Tun farko dai, sabon kontrolan, muhammadu Adamu yace hukumar shige da fice takasa na matukar godiya ga irin tallafi da take samu daga gwamnatin jahar Adamawa, tare da baiwa gwamnati tabbacin cewa jami’an hukumar na shirye domin gudanar da aiki tare da gwamnatin jaha. Yayin da yake kara tabbatar wa gwamnan tsaron jahar, Muhammadu Adamu ya baiwa al’ummar jahar tabbacin ba zasu sake samun matsalar fasfo ba . ganin a yanzu akwai sabon jami’in kula da bada fasfo da aka turo jahar Adamawa kuma ya zo da sabbin dabarbaru da zasu taimaka gurin sauwaka duk wani matsala dake da nasaba da fasfo.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.